1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masifar ambaliyar ruwa a Pakistan

August 2, 2010

An ba da rahotannin ɓarkewar cutar kwalera a yankin ambaliyar ruwan Pakistan

https://p.dw.com/p/OaDW
Hoto: AP

Hukumomi a Pakistan sun tura tawagogin likitoci zuwa arewa maso yammacin ƙasar domin hana ɓarkewar cututtuka masu nasaba da shan gurɓataccen ruwa bayan an ba da rahotannin ɓarkewar cutar kwalera a yankunan dake fama da masifar ambaliyar ruwa mafi muni a tarihin ƙasar. Kawo yanzu mutane kimanin 1100 suka rasu sakamakon wannan bala'i. Gwamnati ta girke dubban ma'aikan ceto waɗanda kawo yanzu sun ceto mutane dubu 28 zuwa tudun mun tsira. To sai dai saboda munin bala'in ya sa mazauna yankunan na ganin tamkar gwamnati ba ta kai wani ɗauki ba. Kuma har yanzu ana cikin ruɗani, inda jiragen sama masu saukar ungulu ke yi ta shawagi a ƙoƙarin taimakawa, kamar yadda wani kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke aikin agaji a yankin ya nunar.

"Mutane sama da dubu 30 sun nemi mafaka akan rufin gidaje, su ne na farko da ya zama dole mu ceto. Muna buƙatar kayan abinci da ruwan sha. Muna fama da matsaloli wajen kaiwa ga mutanen dake buƙatar taimako saboda ruɗanin da ake ciki."

A halin da ake ciki ruwan sama da aka kwashe kwanaki ana yi kamar da bakin ƙwarya ya fara ja, abin da ke bawa hukumomi damar kimanta munin wannan bala'i.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar