1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana farautar rayuwar masu kare muhalli

Abdul-raheem Hassan
September 10, 2024

Wani rahoton kungiyar masu kare hakkin farren hula, ya ce an kashe 'yan fafutukar kare muhalli 200 a shekarar 2023. Rahoton ya ce wasu kasashe na amfani da dokokin kasa wajen murkushe 'yan fafutuka a fadin duniya.

https://p.dw.com/p/4kTJf
'Yar fafutukar kare muhalli, Greta Thunberg
Hoto: Ramon van Flymen/ANP/picture alliance

An kashe kusan masu kare muhalli 200 a duniya a cikin shekarar 2023, kasar Kwalambiya ta sake zama kasa mafi muni ga masu 'yan fafutuka a cewar rahoton Global Witness mai sa ido a duniya.

Rahoton ya kuma nuna fargaba kan yunkurin murkushe masu fafutukar kare muhalli a kasahen Burtaniya da Amirka, rahoton yana mai gargadin cewa ana amfani da dokokin a kasashen wajen yaki da masu fafutuka.

Rahoton na shekara-shekara ya gano Latin Amirka ta kasance yanki mafi hadari a duniya ga masu kare muhalli, wanda ya kai kashi 85 cikin 100i na kisan kai 196 da aka rubuta a bara.