'Yan fafutuka sun soki EU kan muhalli
July 21, 2020Fitacciyar matashiyar nan mai fafutuka wajen kare muhalli Greta Thunberg 'yar kasar Sweden da kuma takwararta Luisa Neubauer ta nan Jamus sun ce gaza samun labari na zage damtse wajen alkinta muhalli bayan zaman da shugabannin Tarayyar Turai din suka yi abu ne maras dadin ji.
A cewarsu, maimakon karkata kan muhalli, shugabannin sun mayar da hankalinsu ne kacokam ga batun da ya shafi tattalin arziki, inda suka ce yin hakan babban hadari ne kuma abu ne mutane da mutanen da ke cikin kasashen EU din ba za su yafe ba.
Gabannin zaman da shugabannin EU din suka yi, wadannan matasa masu rajin kare muhalli sun tattauna da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar Ursula von der Leyen don mika bukatarsu ta sanya batun muhalli a jerin batutuwan da za su zanta a kai.