Masu zanga-zanga na ganin tasku a Togo
September 7, 2017Dubban 'yan kasar Togo sun gudanar da maci a rana ta biyu a kan titunan kasar, 'yan adawar kasar dai na neman da a yi wa kundin tsarin kwaskwarima da za ta kai ga sauke shugaban kasar daga karagar mulki.
Kungiyar kare 'yancin amfani da kafar sadarwar yanar gizo ta Intanet ta kasa da kasa wato Internet Sans Frontiere ta yi tir da Allah wadai da matakin da mahukuntan kasar Togo suka dauka na katse hanyar sadarwar Intanet a kasar. Kungiyar ta bayyana wannan matakin da tauye 'yancin al'ummar Togo na bayyana ra'ayinta ta hanyar yanar gizo.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan adawar kasar ke ci gaba a wannan Alhamis da zanga-zangar nuna kyama da gwamnatin Faure Gnasingbe a duk biranen kasar biyo bayan wacce suka gudanar a ranar Laraba da ta samu halartar mutane sama da dubu 100 a cewar kungiyar Amnesty Internationla ko kuma sama da miliyan daya a cewar 'yan adawar kasar.
Kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa ko a wannan Alhamis ma kafar sadarwar ta Intanet ta kasance a tsinke take. Sai dai ministan sadarwa kana kakakin gwamnatin kasar ta Togo ya ce gwamnati na da hurumin takaice karfin kafar sadarwar Intanet a kasar a bisa dalillai na tsaro.