1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya: Masu zanga zanga sun hallaka

Abdoulaye Mamane Amadou
December 20, 2019

Akalla mutane biyar sun hallaka a Indiya a yayin zanga-zangar da ta sake barkewa ta kin jinin dokar zama dan kasar nan da 'yan kasa da ke haifar da cece-kuce.

https://p.dw.com/p/3VAIo
 No NRC, No CAA movement  Bewegung Proteste Indien
Hoto: DW/S. Bandopadhyay

Sai dai rahotabnnin da ke fitowa daga yankunan da ake zanga zangar na nuni da cewar bayyanan da ake bayarwa na cin karo da juna inda wata majiya ta ce wadanda suka hallaka sun kai 14.

Dubun dubatar mutane sun fito a yau Juma'a 20.12.2019 a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya daya daga cikin jihohin mafi yawan al'umma a karkashin jagorancin jam'iyyar tsohon firaministan kasar Narendra Modi, haka kuma majaiya daga kudancin kasar ta ce mutane da dama sun sake fitowa a wannan rana.

A makon da ya gabata ne majalisar dokokin kasar ta jefa kuri'ar yin na'am da sabuwar dokar ta 'yan cin zama dan kasa, to amma sai dai jama'a da dama suka yi fatali da ita bisa zargin cewa dokar ta mabiya addini Musulunci.