Mata da ke shugabanci a duniya
Akwai kimanin kasashe 195 a duniya kuma mafi akasarinsu maza ne ke jagoranci. Mata kalilan ne ke jagorantar gwamnatocin kasashen duniya amma kuma dukanninsu jajirtattun mata ne.
Sanna Marin
A watan Disambar 2019 ne aka zabi Sanna Marin 'yar shekaru 34 da haihuwa a matsayin firaministar Finland bayan da tsohon firaministan Antti Rinne ya yi murabus. Ms. Marin dai ita ce shugabar gwamnati mafi kankantar shekaru a duniya. Gabannin hawa wannan matsayi, ta rike mukamin ministar sufuri ta kasarta ta Finland.
Jacinda Arden
Tun cikin watan Oktoban 2017 ne Jacinda Arden ke rike da mukamin firaminista a kasar New Zealand kuma ita ce mutum ta 40 da ta dare kan wannan mukami. Ta hau wannan matsayi ne a lokacin da take shekaru 37 da haihuwa. Ita ce mace ta farko da ta rike shugabancin kasa. Ana daukar Arden a matsayin guda daga cikin jajirtattun mata da ke shugabanci.
Jeanine Anez
Bayan murabus din da shugaban Boliviya Evo Morales ya yi a watan Nuwamba, Jeanine Anez mai shekaru 52 da haihuwa ta kasance shugabar kasar ta rikon kwarya. Gabannin hawa kan wannan kujera, Anez ce ke rike da mukamin mataimakiyar majalisar dattawan kasar. Burinta yanzu shi ne shirya zabe karbabbe nan ba da jimawa ba.
Sophie Wilmes
Bayan da ta rike mukamin ministar kasafin kudin kasar Beljiyam, Sohpie Wilmes ta zama firaministar kasar kuma ita ce mace ta farko da ta rike wannan mukami. 'Yar shekaru 44 da haihuwa, Ms. Wilmes, na da jan aiki a gabanta na daidaita lamura a majalisar dokokin kasar.
Zuzana Caputova
Al'ummar Sulobakiya sun zabi Zuzana Caputova a matsayin mace ta farko da za ta shugabanci kasar a farkon shekarar 2019. Shekarun ta 45 da haihuwa a lokacin da ta dare kan wannan kujera ta shugaban kasa. Ms. Caputova ta yi fice wajen rajin kare muhalli da kuma kokari wajen kawar da cin hanci a kasar. Ba ta taba rike wani mukami na siyasa ba gabannin samun wannan matsayin na shugabar kasa.
Angela Merkel
A shekarar 2005 ce aka zabi Angela Merkel a matsayin shugabar gwamnatin Jamus. 'Yar shekaru 65 da haihuwa, Ms. Merkel ce mace ta farko da ta hau wannan kujera. Yanzu haka tana wa'adinta na hudu ne wanda zai kare a shekarar 2021 kuma ta ce ba za ta nemi wani sabon wa'adi ba. Merkel dai 'yar gabashin Jamus ce kuma mahaifinta limamin addinin kirista ne.
Sahle-Work Zewde
Majalisar dokokin kasar Habasha ta zabi Sahle-Work Zewde a matsayin shugabar kasa wadda ita ce ta biyar da ta riki wannan matsayin kana mace ta farko da aka zaba. A halin yanzu dai ita ce shugabar kasa mace daya tilo a Afirka. Gabannin hawa wannan kujera, shugabar 'yar shekaru 69 ta yi aiki a matsayin jami'ar diflomasiyya inda ta rike mukamai da dama a Majalisar Dinkin Duniya.
Tsai Ing-wen
Tsai Ing-Wen ce mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar kasa a Taiwan. A shekarar 2016 ce aka rantsar da ita, batun da ya jawo takun saka tsakanin Taiwan din da China kan cin gashin kan Taiwan. Tsai ta bayyana cewar ba za ta taba amincewa da duka wata matsin-lamba da za a yi mata ba kan 'yancin Taiwan din. Ta bayyana cewar za ta sake neman shugabancin Taiwan din a shekarar 2020.
Erna Solberg
Norway ma dai a halin yanzu na karkashin jagorancin mace ne. A shekarar 2013 Erna Solberg 'yar shekara 58 ta dare kan gadon mulki. Ita ce mace ta biyu da ta riki wannan mukami. Tsauraran matakan da ta dauka kan karbar baki na daga cikin abubuwan da suka sanya ake mata lakabi da "Iron Erna." Shugabar dai ita ce ke jagorantar jam'iyyar Conservative ta kasar ta Norway.
Saara Kuugongelwa-Amadhila
Saara Kuugongelwa-Amadhila ce firaministar kasar Namibiya ta hudu. Tun cikin shekarar 2015 take rike da wannan matsayi. Kuugongelwa-Amadhila ta yi zaman gudun hijira a kasar Saliyo lokacin da take da kankantar shekaru. Ta yi karatunta na gaba da sakandare a Amirka inda ta samu digiri a fannin tattalin arziki kafin ta koma gida a shekarar 2014. Ita ce mace ta farko da ta hau wannan matsayi a kasar.
Sheikh Hasina
Sheikh Hasina ce firaminista ta 10 kana wadda ta fi jimawa kan wannan matsayi a tarihin kasar Bangladesh. Kafin fara wannan wa'adi cikin shekarar 2009, Sheikh Hasina ta riki wannan matsayi tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001. Mujallar nan ta Forbes ta bayana shugabar 'yar shekaru 72 da haihuwa a matsayin daya daga cikin mata 100 fitattu a duniya a shekarar 2016 da 2017 da kuma 2018.
Kolinda Grabar-Kitarovic
Gabannin zamanta shugabar Croatia a shekarar 2015, Kolinda Grabar-Kitarovic ta rike mukamai da dama sannan ta kasance jakadar kasarta a Amirka. Ms. Grabar-Kitarovic ce mace ta farko da ta riki wannan mukami. Matsayin da ta rike na mataimakiyar babbar sakataren kungiyar tsaro ta NATO kan huldar diflomasiyya ya sanyata kasancewa mace ta farko da ta rike wannan mukami a tarihin kungiyar.