Mata sama da 60 aka ci zarafinsu a 2015
March 4, 2016Wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a ranar Alhamis ya nunar da cewa an samu dakarun kwantar da tarzoma na majalisar su 69 da aikata ayyukan lalata a lokacin wasu aikace-aikace 10 da dakarun suka fita a shekarar 2015.
Mafi akasarin dakarun da aka samu da aikata wannan lalata dai sun fito ne daga kasashen Afirka. A cewar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon rabi na ayyukan lalatar da dakarun suka aikata ya faru ne a kasashen jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kasar Kongo.
Dakarun dai da ake turawa aikin kwantar da tarzoma ana zargin na bigewa da aikata lalata da mata suna basu kudi koma yin fyade ga kananan yara. Babu dai koda jami'i daya cikin wadannan dakaru da ya fiskanci hukunci mai tsananin saboda laifin na shekarar bara.
A cewar rahoton dai da ke fita a ranar ta Alhamis a kwai bukatar tsaurara matakan da ake dauka kan binciken wannan ta'asa, ciki kuwa har da bukatar yin gwajin kwayoyin halitta na DNA dan gano wadanda ake zargi da aikata laifukan.