1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata sun fi tserewa yakin Ukraine

April 4, 2022

Alkalumman ma'aikatar cikin gida ta nan Jamus ya tabbatar da cewa kaso hudu cikin biyar na 'yan gudun hijirar da suka tserewa yaki a Ukraine mata ne.

https://p.dw.com/p/49S5e
Mexiko | Ukrainische Flüchtlinge in Tijuana
Hoto: Mario Tama/AFP

Rahotannin na nuni da cewa tun bayan da Rasha ta kaddamar da yaki a kasar Ukraine, aka haramtawa maza masu shekaru 18 zuwa 60 fita daga kasar.

A kididdigar da Jamus din ta gudanar, kimanin kashi 90 na 'yan gudun hijirar da kasar ta karba a yanzu mata ne wadanda suka tsere tare da 'ya'yansu. A halin yanzu dai Jamus ta yi rijistar fiye da 'yan gudun hijirar Ukraine dubu dari uku yayin da ake hasashen ta yiwu adadinsu ya karu saboda dokar da ta bai wa 'yan Ukraine din damar zama a Jamus na tsawon kwanaki 90 ba tare da takadar izinin Visa ba.