Nijar: Martani kan janye tallafin haihuwa
December 21, 2021Iyaye matan dai na cewa matakin gwamnatin ya rusa duk fafutukar da hukumomi da kungiyoyin kula da lafiya suka yi da lokacin da aka bata na wayar da kan mata game da muhimancin haihuwa a asibiti, wanda hakan ka iya dawo da al'adar nan ta haihuwa a gida. Shi dai wanan tallafi da matan ke samu yayin haihuwa da a yanzu gwamnatin kasar ta aiwatar da matakin da dakatar da shi, kwarya-kwaryan tallafi ne da wata kungiya ta bullo da shi a jihohi bakwai na kasar.
Tallafin dai na zaman gwaji na tsawon shekara guda, wanda mata daga na birane zuwa karkara suka yi marhabin da shi musaman mata masu karamin karfi da a baya haihuwa a asibiti ya kasance musu alakakai. A cewar gwamnatin kasar ta bakin ministan kiwon lafiya, tallafin da ake batu bai shafi tiyata da awon ciki da awon yaro da magungunan da ake bai wa yara 'yan kasa da shekaru biyar na sha ka tafi da kuma magungunan ciwon daji ba.