Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus ya ziyarci Ukraine
April 3, 2023Talla
Da safiyar Litinin din nan ne dai matamakin shugaban gwamnatin na Jamus, Robert Habeck tare da rakiyar wata tawagar 'yan kasuwa suka isa Ukraine din, za kuma ta maida hankali kan sake gina Ukranie din da kuma hadin kai musamman a bangaren makamashi.
Babban jami'in na Jamus Mr. Habeck wanda har ila yau ke ministan kula da harkokin tattalin arziki ya bayyanan ziyarar a matsayin ta bai wa Ukraine da ke fama da yaki kyakkyawar fata.
Tafiyar da aka yi ta jirgin kasa, ita ce ta farko da mataimakin shugaban gwamnatin na Jamus ke yi zuwa Ukraine tun bayan da Rasha ta afka mata da yaki a ranar 24 ga watan Fabrairun bara.