1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan kare muhalli a kasar Ghana

October 7, 2015

Shara da gurbata muhalli ya zama babban kalubale a Ghana, a don haka ne kungiyar “Hipsters of Nature” ta dukufa wajen wayar da kan jama'a don samun mafita.

https://p.dw.com/p/1Gjt7
DW - Africa on the move
Hoto: DW

Kungiyar mawaka ta “Hipsters of Nature” na son a shigar da batun kare muhalli cikin zamantakewar jama'a ta hanyar kwashe kwalaben robobi don sake sarrafasu, da ma ilmantar da 'yan makaranta kan yadda za su rarraba shara. Suna kuma shirya wasannin kade-kade da gasar sanya tufafi don samun goyon baya.

Wannan matsala ta yawaitar juji a Accra babban birnin kasar Ghana dai, a yanzu ta soma ci wa 'yan kasar tuwo a kwarya ganin yadda bolar ke toshe magudanar ruwa da ka iya jawo ambaliyar da ta ritsa da mutane da dama a watannin baya.

Beatrice Dossah ta kungiyar "Hipsters of Nature" na daga cikin wadanda ke takaicin halin da kasar ke ciki, wadda kuma ke ganin rashin daukar mataki ka iya jefa al'umma cikin wani hatsari.

“Idan ba mu daina wannan halayya ta zubar da shara ko-ina babu kakkautawa ba, ba mu kuma samu hanyar magance ta ba, mutane za su yi ta fama da ambaliyar ruwa. Ba ma son wani rai ya sake salwanta saboda ambaliya.”

Mafita daga matsalar gurbata muhalli

Shekaru uku baya ne dai Beatrice Dossah ta kafa kungiyar "Hipsters of Nature", don neman mafita da ma shawo kan mutane su kare muhalli, inda suke fatan ganin matasa sun dage wajen kare muhalli a makarantu.

DW - Africa on the move
Wasan kwaikwayo don kare muhalliHoto: DW

Daya daga cikin daliban wato Memuna Ibrahim ta yaba da wannan yunkuri da ake koya masu.

„Sun nuna mana cewa mu kare muhallin mu. Domin idan ba mu kare muhallinmu ba, muna iya kamuwa da cuta har ma mu mutu.“

Wannan kungiya dai na shirya gangami a makarantu daban-daban da nufin koya wa yara yadda za su sarrafa tufafi da ma wasu abubuwan amfani da ga irin robobin da aka yi amfani da su, wanda kuma ya samu karbuwa hatta ga iyayen daliban.

Neman tallafi don kare muhalli

To sai dai fa kungiyar "Hipsters of Nature" ba ta samun wani tallafi kan ayyukan kirkire-kirkire da suke yi. To amma tana samun agaji daga Helen List, wata 'yar Austreliya da ke da otel a gabar tekun Accra, inda suke kwashe shara a gabar tekun da ma sauran magudanar ruwa da ke yankin.

"Kwastamomi na ba sa iya zuwa ninkaya a nan wurin. Yanayin wurin ya canja ba shi da sha'awa idan ka hango shi daga gidan abinci ne wato resturant. Yayi mummunan tasiri kan harkar kasuwanci na.”

A baya-bayan nan ne masu fafutukan da yaran makaranta suka yi bikin ranar kare muhalli ta duniya a Otel din Helen List. A yanzu dai Beatrice Dossah da Helen List suna shirin hada hannu don jawo hankalin mahukuntan kasar wajen yaki da gurbatar muhalli.