Kokarin shawo kan rikicin da ya addabi Siriya
December 11, 2015Assad ya bayyana hakan ne a wannan Jumma'a yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasar Spain EFE inda ya ce tun bayan da yaki ya barke a kasar sun nemi tattaunawa da dukkan bangarorin da ke cikin rikicin, koda ya ke ya ce akwai ban-banci tsakanin 'yan adawa da 'yan tawaye ko 'yan ta'adda wadanda ya ce ba zai taba hawa kan teburin sulhu da su ba. Matakin na Assad dai na zuwa ne kwana guda bayan da suma 'yan adawan a nasu bangaren, a yayin wani taro da suka gudanar a birnin Riyadh na kasar Saudiya, suka ce a shirye suke su shiga cikin tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta bukata a kan rikicin waddda za a yi da gwamnatin Siriyan karkashin jagorancin Bashar al-Assad din. Assad ya bayyana cewa a shirye yake ya tattauna da bangaren 'yan adawar kasar da suka halarci taron na Riyadh a wani mataki da ke nuni da kawo karshen rikicin Siriyan ta hanyar siyasa. Sama da shekaru biyar kenan dai da Siriyan ta tsinci kanta a cikin yakin da ya dai-daita ta.