Matakan rage yaduwar cutar daji
February 4, 2014Ranar 4 ga watan fabrairun kowace shekara rana ce da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ware a matsayin ranar fadakar da jama'a a kan illar cutar cancer ko daji ga bil'adama. Cutar da kuma hukumar ta lafiya ta ce ta na kashe akalla mutane kusan miliyan 8 a duk shekara.
Matsalar cutar cancer ko kuma daji a hausance, cuta ce da ta gagari likitoci da sauran masana harkokin lafiya a duniya. To sai dai kuma wannan bai hana likitoci da sauran masu dauke da wannan cuta neman magani da kuma bayanai na hana kamuwa da wannan cuta ko kuma maganinta ba a tsakanin bil'adama, kamar yadda babban sakatare a hukumar kula da asibitoci a jihar Naija Dr Muhammad Muhammad Makunsidi ya shaida ma ni:
"Shi cancer da ma ya kan fito ne kamar kurji ko kumburi, yawancinsu, amma ba wai dole sai ya zama kumburi ba, ma'ananshi shi ne, idan wuri ya jimu, idan ya warke zai daina toho. To shi cancer sinadarai ne a cikin jikin mutun kuma sashen jikin mutun ne, wanda maimakon ya daina toho sai ya rika toho ba kai ba gindi, ya zama ya na matse wuri ko kuma ya hana wasu sashen jiki aiki yadda ya kamata. Idan aka tarbe shi yana fitowa, to gaskiya ana iya samun warkarwa amma idan ya yi nisa to sai dai mutuwa"
Matsalolin da cutar ke haddasawa
Cutar dai ta cancer cuta ce dake lakume makudan kudade bayan zaman tararrabi da take saka mai jinyan da kuma yan uwansa a ciki, kamar yarda Malam Abdullahi da shi ma yayi jinyan yar uwarsa daga bisani kuma ya rasata ya shaida ma ni
"Ita dai wannan cuta wanda ake ce wa cancer, cuta ce wadda idan ta sami wani danuwanka ko wani naka, ba karamin tashin hankali ba ne, haka muka yi ta fama daga wannan asibiti zuwa wancan, banda ma maganinshi ga shi da tsada, a je kuma a yi ta yin na gargajiya a dawo a yi na bature, ga wahalarwa, ga kuma ɗaukar lokaci. Ka yi ta fama, gobe a yi nasara, jibi a yi nasara, daga karshe dai ita wannan 'yar uwar tawa dai Allah ya ɗauke ranta"
Wata matsalar da masana kiwon lafiya ke fuskanta wajen shawo kan wannan cuta musanman a kasashe masu tasowa irin su Najeriya itace ta rashin fadakarwa da kuma jahiltar wannan cuta, inda ake cewa bata jin maganin asibiti, hasashen da kuma Dr Makunsidi ya musanta
"Rahsin illimin ke nan domin shi ya sa ma ake ci mi shi ciwon daji idan ka je ma aka yi maka allura ai sai mutuwa, amma ba haka ba ne, shi ciwon dajin kamar yadda na fada, in dai aka samu aka je tun da wuri, akan yanke bakin, dan shi maganin cancer ya kasu kashi-kashi, da fari dai zai bukaci mutane a fannoni daban-daban da suka shafi maganinsa sanan akwai wanda ake hadiyewa, ba dole sai an yi operation ba, domin ya warkar da ciwon, akwai kuma radiation, wato radiotheraphy, shi kuma za'a haskaka wata naura ce ta kona bakin inda cancer take, ko kuma a yanke bakin wurin."
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Pinaɗo Abdu Waba