1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan shawo kan Iran game da nukiliya

May 23, 2012

Iran na shan matsin lamba daga ƙasashen duniya da ke faɗa a ji game da da shirinta na inganta makamashin uranium da aka daɗe ana taƙaddamar akai.

https://p.dw.com/p/151Hp
Fotomontage *** Image #: 7210130 The Bushehr nuclear power plant is seen the Bushehr Port on the Persian Gulf, 1,000 kms south of Tehran, Iran on February 25, 2009. Iranian officials said the long-awaited power plant was expected to become operational last fall but its construction was plagued by several setbacks, including difficulties in procuring its remaining equipment and the necessary uranium fuel. UPI Photo /Landov
Hoto: dpa/landov/Montage: DW

Manyan ƙasashen duniya na ci gaba da matsa wa Iran lamba domin ta yi watsi da shirin da suke zarginta da neman aiwatar na neman ƙera makamin ƙare dangi a asirce. Wani kakakin kantomar harkokin wajen gamayyar Turai Catherine Ashton ya bayyana cewa ƙasashe biyar da ke tattaunawa da Iran sun sake miƙa mata wata sabuwar shawara. Ba a dai bayyana takamaimen abin da tayin nasu ya ƙunsa ba, amma kuma ya ce bakin ƙasashen Amirka, da Birtaniya, da Faransa, da Rasha, da china da kuma Jamus ya zo ɗaya game da hanyoyin da ya kamata a bi domin warware wannan taƙaddamar nukuliyar Iran cikin ruwan sanyi.

A cewar wakilin ƙasar Iran a tattaunawar da ta gudana a birnin bagadaza na Iraƙi, gobe ne idan Allah ya yarda za a koma kan teburin fahimtar juna game da shirin na inganta uranium. Ƙasashen yammacin duniya sun nunar da cewar Iran na fakewa da shirinta na inganta uranium wajen samar da makamin ƙare dangi. Sai dai hukumomi Teheran na ci gaba da kare kansu inda suka zargin ba shi da tushe da kuma makama.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal