Matakan sulhu a rikicin Ukraine
December 24, 2014An soma wata tattaunawar zaman lafiya da ke da muradin ganin an samar da sulhu tsakanin dakarun sojan gwamnati da 'yan aware masu samun goyon bayan Rasha a yau Laraba.
Cikin batutuwan da ake son tattaunawa a kansu akwai batun janye manyan makaman yaki da musayar firsinonin siyasa.
Da yammacin yau ne dai wakilai daga bangarorin na Rasha da Ukraine da na kungiyar hadin kan tsaro a tsakanin kasashen Turai dana 'yan aware suka hallara a wurin tattaunawar wato Belarus. Ba a dai bar kafafan yada labarai ba kaiwa ga ginin gwamnatin da ake wannan tattaunawa.
Nan gaba kuma a ranar Juma'a za a sake wata tattaunawar wacce Valeriy Chalyi, mataimakin shugaban ma'aikata a gwamnatin kasar ta Ukraine ke cewa a ranar ce zaa ji cikakken sakamakon tattaunawar.