1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin Girka na tangal-tangal

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 29, 2015

Mahukuntan kasar Girka sun bayar da umurnin rufe bankunan kasar a wannan Litinin din tare da fara gudanar da binciken kudaden da masu ajiya a bankuna suka mallaka.

https://p.dw.com/p/1FonF
Al'ummar kasar Girka na rububin daukar kudi a mashin din ATM
Al'ummar kasar Girka na rububin daukar kudi a mashin din ATMHoto: picture-alliance/dpa/A. Vlachos

Hukumar kula da kudaden kasar Girkan dai ta bayar da umurnin rufe injinan daukar kudi a banki da ake kira da ATM tare da kayyade adadin kudin da za a iya dauka bayan an sake budesu zuwa Euro 60 kacal a rana. A hannu guda kuma a wata hira da gidan telibijin din kasar ya yi da Firaminista Alexis Tsipras duk da cewa ya ki cewa komai a kan hutun da bankunan suka tafi, ya ci gaba da jaddada cewa babu wata matsala da za ta shafi kudaden mutanen da ke ajiye a bankunan da kuma kudaden albashi da fansho. A wannan Talatar ce dai wa'adin da aka dibar wa mahukuntan na Athens na biyan bashin da Ausun ba da Lamuni na Duniya IMF ke binsu na sama da biliyan daya na kudin Euro ke cika.