Matakan yaki da maleriya a duniya
April 25, 2019Talla
Yayin da ake bikin ranar yaki da zazzabin cizon sauro ta bana a waje guda kuma ana muhawara kan tasirin amfani da maganin da ake sarrafawa da itaciyar da aka fi sani da Artemesia wajen warkar da cutar.
Sai dai kamfanin dake sarrafa maganin na Artemesia wanda ke da rassa a wasu kasashen Afirka da kuma ya share shekaru biyar yana tallata wannan magani yace yana da yakini maganin yana warkar da cutar ta maleriya.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi kiyasin cewa cutar maleriya na halaka mutane 435,000 a kowace shekara a nahiyar Afirka kadai.