Amirka za ta rage tiririn da take fitarwa
April 22, 2021A ranar ashirin da biyu na kowacce shekara ake bikin alkinta muhalli, Shugaban Amirka, Joe Biden ya dauki alkawarin rage yawan hayakin da kasar ke fitarwa, a kokarin da Amirka da sauran manyan kasashen duniya ke yi, na ganin an ceto duniya daga barazanar dumamar yanayi. Taron na kwanaki biyu da ke gudana ta kafar bidiyo saboda annobar corona, ya sami halartar shugabanin kasashen akalla arba'in. Biden zai yi kokarin nusantar da sauran takwarorinsa kan illolin fitar da yawan iskar gas mai dumama yanayi ga tattalin arziki da lafiyar al'ummar duniya.
Amirka a yayin tsohuwar gwamnatin Barack Obama ta yi alkwarin rage tiririn da ke dumama yanayi da take fitarwa da kashi ashirin da takwas amma gwamnatin Biden ta shirya ninka shi zuwa kashi hamsin zuwa hamsin da biyu nan da shekarar 2030. China da Brazil na sahun gaba a fitar da hayakin da ke gurbata yanayi. Masana dai na cewa amfani da bakin gawayi wurin samar da lantarkin da China ke yi, shi ne mafi hadari ga muhalli a cikin hanyoyin da ake samar da lantarki a duniya.