Matakin Amurka a Afrika ta Tsakiya
December 28, 2012Amurkan ta ce daukar wannan matakin ba wai ya na nufin lalalcewar dangantaka da Jamhuriyar ta Afrika ta Tsakiya ba ne, wani yunkuri ne in ji Amurkan na kare al'ummarta da ke kasar a saboda haka ne ma ta gargardi Amurkawa da su gujewa shiga kasar a dan tsaknin nan saboda abubuwa da ka je su komo.
Ita ma dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce kwashe wasu daga cikin jami'anta daga Jamhuriyar ta Afrika ta Tsakiya saboda halin da ta tsinci kanta a ciki.
Tuni dai shugaban kasar Francois Bozize ya yi kira ga Amurka da Faransa da su agaza masa wajen dakile 'yan tawayen wanda yanzu haka ke kokari danna kai babban birnin kasar domin karbe iko da shi, sai dai Faransa ta ce ba za ta bada wani agaji na soja ba.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammed Awal Balarabe