1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin Eu a kan Kungiyar Hezbollah

July 22, 2013

Kungiyar Gamayyar Turai ta sanya reshen Hezbollah da ke dauke da makamai a matsayin kungiyar da ke gudanar da ayyukan ta'addanci a duniya.

https://p.dw.com/p/19Brg
Lebanese Shiite Muslim Hezbollah militants ride on a vehicle carrying a Fajr 5 missile during the annual parade in the southern town of Nabatiyeh on November 28, 2012, to mark the 13th day of Muharram on the Islamic calendar, commemorating and mourning the seventh-century martyrdom of Prophet Muhammad's grandson, Imam Hussein, in the battle of Karbala in Iraq. AFP PHOTO/MAHMOUD ZAYYAT (Photo credit should read MAHMOUD ZAYYAT/AFP/Getty Images)
Hezbollah ta saba nuna makamantaHoto: Mahmoud Zayyat/AFP/Getty Images

Ministocin harkokin wajen Eu ne suka yanke wannan hukunci a taron da suke gudanarwa a birnin Bruxelles, shakara guda bayan harin da 'yan bindigan Hesbollah suka kai a filin saman Burgas na Bulgariya a ranar 18 ga watan Yulin 2012.

Mutane da dama ne suka kwanta da dama a wannan hari ciki kuwa har da dan Bulgeriya daya, da kuma 'yan Isra'ila biyar. Ko da shi ma ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, sai da ya ce bai kamata a kyalle reshen kungiyar Hezbollah da ke dauke da makamai ya aiwatar da hari a wata kasa ta nahiyar Turai ba tare da daukan mataki a kanta shi ba.

Kungiyar ta Gamayyar Turai ta kuma haramta wa jami'an masana'antu da kuma kungiyoyi da ke da alaka da Hezbollah shigowa nahiyar Turai tare kuma da toshe kafofinsu na ajiyan kudi a bankunan Turai.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh