1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin EU na kare martabar kudin Euro

October 26, 2010

Ministocin EU na nazari ko ya dace a yi gyara ga kundin tsarin mulkin kungiyar.

https://p.dw.com/p/Po32
Tutocin kasashen tarayyar turaiHoto: AP

Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar tarayyar turai wadanda ke gudanar da taro a Luxemburg sun yi ta zazzafar muhawara a game da batun ko ya dace a yiwa kundin tsarin mulkin kungiyar kwaskwarima kasa da shekara guda bayan da kasashen suka rattaba hannu akan daftarin kundin tsarin mulkin. Ministocin na nazari ne domin samo hanya mafi dacewa ta kare martabar kudin euro da kuma kaucewa fadawa matsalar tattalin arziki yadda idan daya daga cikin kasashen ta sami kanta cikin matsalar tattalin arzikin ba zai durkusar da dukkanin kasashen nahiyar ba. Kasashen Faransa da Jamus na masu ra'ayin cewa dukkan kasar da ta karya ka'idar gibin kasafin kudi, ya kamata a dakatar da ita na wani lokaci. Sai dai kuma daukar wannan mataki na nufin sake yin gyara ga daftarin kundin tsarin mulkin wanda kungiyar ta sha wahala kafin ta samar da shi. Ministan harkokin wajen Austria Michael Spindelegger yace Jamus da Faransa ba zasu sami cikakken goyon baya daga sauran kasashe ta sauya kundin tsarin mulkin ba.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu