Jamus: Sabon takunkumi kan Iran
January 21, 2019Wasu kafafen yada labaran kasar ta Jamus da suka hadar da Jaridar Süddeutsche Zeitung da gidajen radiyon NDR da WDR, sun ruwaito cewa hukumar kula da harakokin sufurin jiragen sama ta kasar ta Jamus ta dakatar da lasin aiki ga kamfanin jiragen sama na Mahan Air na kasar ta Iran wanda ke aikin jigilar fasinjoji daga filin jiragen sama na Tehran zuwa filayen jiragen sama na biranen Düsseldorf da Munich.
A makon da ya gabata ne dai Hukumomin shari'a a Jamus suka sanar da kama wani mai bai wa rundunar sojojin kasar shawara, bisa zargin yin leken asiri ga kasar Iran din. Jamus na zargin mutumin Abdul Hamis S mai shekaru 50 a duniya da ke da takardun dan kasa na kasashe biyu Jamus da Afganistan da yin amfani da matsayinsa na mai bayar da shawara kan harakokin al'adu da yaruka a rundunar sojojin kasar ta Jamus, domin bayar da wasu bayanan sirri ga hukumar leken asirin kasar Iran.