Kara neman saukaka zubar da ciki a Jamus
January 23, 2025A Jamus ayar doka mai lamba 218 da aka samar da ita sama da shekaru 150 ka iya kai mace gidan yari har na tsawon shekaru uku ko ma a ci tarar ta idan aka sameta da laifin zubar da ciki ba tare da bin wasu ka'idoji, duk da cewar akwai haramci kan zubar da ciki a kasar ta Jamus, tun daga farkon shekarar 1990 mata za su iya aiwatar da shi kafin ya shiga watannin farko ba tare da sun fuskanci fushin doka ba bisa wasu sharudan da ke nuna rayukansu ko ma kwakwalwarsu na cikin hadari ko kuma bayan an yi musu fyade.
Karin Bayani: Shugaban gwamnatin Jamus zai sake tsayawa takara
To sai dai wannan ayar dokar ta 218 da ake ci gaba da cece-kuce a kanta a daukacin kasar ba wai a kan mata kawai ta tsaya ba, likitoci da suka taimaka a ka zunar da ciki ka iya rasa aikinsu kazalika dalibai masu koyon aikin likitanci yanzu haka ba a koyar da su yadda ake gudanar da wannan aiki. Tun daga shekarar 2003 likitoci da asibitoci da ke taimakawa mata zubar da ciki sun ragu da kusan rabi, lamarin da ke matukar wahala musamman a sassan kudancin kasar.
Ulle Schauws yar jam'iyyar the greens masu rajin kare muhalli da kuma Carmen Wegge yar jam'iyyar SPD kokarin kawo karshen wannan doka nan da karshen zaman majalisa kafin zabe. Daga cikin abubuwan da wadannan mata ke adawa da shi akwai bukatar zama na tattaunawa da masana sau uku kafin mace ta sami damar zubar da ciki, wadannan matan na ganin wannan mataki na tilsatawa mata neman shawarwari daga wasu da ba danginsu ba yana cin karo da yancinsu.
Shugaban gwamnati Olaf Scholz wanda ya saka hannu a kan kudirin, inda ya janyo kakausar suka musamman daga bangaren abokan hamayyarsa.
Akwai yiwuwar adawa mai zafi ta taso a kan wannan batu, kuma ba kawai daga bangaren jam'iyyun CDU da CSU ba har ma daga bangaren dama, jam'iyyar AFD mai kyamar baki a shirinta na zabe ta dauki matsayin bayar da fifiko ga dan da ke ciki tare da yin watsi da duk wani tallafi na jihohi kan batun zubar da ciki.
Sabbin shawarwarin jam'iyyun SPD da Greens na samun goyon bayan masu tsatsauran ra'ayi, wadanda suka bukaci a cire sakin layi na 218 daga cikin kundin laifuka da kuma samar da rigakafin hana haihuwa kyauta, ta ce matsalolin da ake samu a yanzu basu dace da yancin mata na cin gashin kansu ba.