1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta dauki matakin shigar da Sweden cikin NATO

Suleiman Babayo MA
January 22, 2024

Majalisar dokokin Turkiyya za ta kada kuri'ar shigar da Sweden cikin kungiyar tsaron NATO.

https://p.dw.com/p/4bZ0e
Birnin Ankara | Majalisar dokokin Turkiyya
Majalisar dokokin TurkiyyaHoto: /Burhan Ozbilici/AP/picture alliance

Ana sa ran majalisar dokokin kasar Turkiyya za ta tattauna batun shigar da kasar Sweden cikin kungiyar tsaron NATO ko OTAN, kamar yadda majiyoyin majalisar suka tabbatar. Tuni kwamitin majalisar mai kula da harkokin waje ya amince da matakin na kada kuri'ar shigar da kasar ta Sweden domin zama mamba a kungiyar tsaron mai matukar tasiri.

An samu tsaikon kimanin shekara guda, kuma da zarar majalisar dokokin Turkiyya ta amince da shigar da Sweden a mastayin mamba na NATO, wanda majalisa take da damar, matakin na gaba sai kasar Hangari wadda ta ce sai Turkiyya ta amince kafin majalisar dokokin ta Hangari ta kada kuri'ar amincewa. Kasashen Yammacin Duniya suna goyon bayan shigar da Sweden cikin kungiyar ta NATO.

Kasashen Sweden da Finland sun bukaci shiga kungiyar tsarin NATO bayan kutsen da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, kuma tuni aka amince da matakin shigar da Finland cikin kungiyar ta NATO.