1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Ukraine na kokarin yin sulhu

Zulaiha Abubakar
September 7, 2019

Shugaban kasar Ukraine Volodymr Zelensky ya bayyana musayar firsinonin da ta gudana tsakanin kasarsa da Rasha, a matsayin matakin farko na shirin kawo karshen rashin jituwar da ke tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3PDWk
Ukraine Kiew Gefangenenaustausch mit Russland Präsident Wolodymyr Selenskyj
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Lukatsky

Anyi musayar firsinonin da yawansu ya kai 70 bayan da jirgin kowacce kasa dauke da firsinoni 35 ya sauka a filayen jiragen saman kasashen. Dangantaka dai ta yi tsami ne tsakanin kasashen biyu, tun a shekara ta 2014, inda har yankin Crimea da ke kasar Ukraine din ya kada kuri'ar raba gardama tare da ballewa ya koma karkashin ikon Rasha.

Yanzu haka dai kasar Faransa ta bukaci shugabannin kasashen Jamus da Rasha da kuma Ukraine din da su sake hawa teburin tattaunawa domin tabbatuwar sulhun da aka fara cimma.