1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauya salon buridi a Kamaru saboda karancin alkama

Mouhamadou Awal Balarabe SB)(ZMA
April 12, 2022

A kasar Kamaru, yayin da farashin biredi ke kara hauhawa sakamakon karancin garin alkama, wata dabara ta cikin gida ta sa samun saukin matsalar inda wani matashi dan kasuwa a kudancin kasar wata dabara.

https://p.dw.com/p/49qa5
BG Putins Ressourcen-Krieg gegen die Welt
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images

A kasar Kamaru, yayin da farashin buredi ke kara hauhawa sakamakon karancin garin alkama, wani dabara ta cikin gida ta sa a samu saukin matsalar wannan kayyayaki a cikin watan Ramadan. Wani matashi dan kasuwa mai suna Claude Ewoty da ke zaune a Ebolova a Kudancin Kamaru, ya fara samar da garin rogo wajen maye gurbin filawar alkama.

Amfani da garin rogo wajen yin burudi ya zama gobarar Titi a Kamaru sakamakon tashin farashin garin alkama biyo bayan mamaye Ukraine da Rasha ta yi. Hasali ma Ernest Claude Ewoty ya bullo da wata dabara ta sarrafa bawon rogo zuwa gari. Ya bayyana yadda tunanin amfani da bawon rogon ya zo masa, inda ya ce wani lokacin a wata unguwa ya iske wata tana bare rogo, sannan ya bukaci bawon rogon, daga bisani ta tambaye shi ko dabbobi zai bai wa, sa ya ce mata dama ce a gare shi na ganin yadda zai sarrafa bawon rogo zuwa garin rogo ko filawa.

Symbolbild Äthiopien Ankunft des Konvois mit Hilfslieferungen in Tigray
Hoto: Amanuel Sileshi/AFP

A halin yanzu dai kasar Kamaru na fama da matsalar karancin garin alkama. Buhun filawa mai nauyin kilogiram 50, wacce a da ake sayar da ita ce CFA 16,000, yanzu ya kai CFA 24,000, ko ma fiye da haka. Saboda haka ne matashin dan kasuwan ya yi imanin cewa wannan ita ce mafita ta farko ga wannan matsala ta karancin filawa.

Garin rogon da ake samu yanzu haka bai taka karya ya karya ba, amma cibiyar tattalin arziki da bunkasa dangantakar kasuwa ta kamaru tallafa wa Claude don kara habaka yawan garin rogon da yake samarwa, kamar yadda Blanche Bikoum manajan cibiyar ta bayyana dabarar a matsyin karfin gwiwa.

Yankin kudancin Kamaru dai wata babbar cibiyar noman rogo ne, lamarin da ya sa ake fitar da shi zuwa kasashe makwabta kamar Gabon da Equatorial Guinea. Amma Ernest Claude Ewoty, wanda ya zuwa yanzu yana gudanar da ayyukansa da kudadensa, yake fatan samun tallafin gwamnati domin bunkasa aikinsa domin samar da burudi a farashi mai rahusa.