Sarrafa nau'o'in hatsi wajen samar da gari
June 24, 2020Rufe Makarantu da gwamnati ta yi sakamakon cutar Corona ya dauki hankalin wani matashi da ke karatun likita a jami'ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto, inda ya soma sarrafa masara, dawa, da kuma gyada wajen samar da gari ga mabukata.
Shi dai wannan matashi Abubakar Rimi dama dai yana ajin karshe ne a sashen koyar da aikin likitanci, duk da yake bai jima da soma wannan sana'ar ba, amma kuma ba tare da bata lokaci ba ya bude kamfaninsa mai sunna Umman Nutri Mix, inda yake sarrafa waken soya, gero, dawa, masara, da kanunfari zuwa gari.
Yajin aiki da aka tafi na malaman jami'o'i da kuma dokar kulle da aka dauka don dakile yaduwar cutar Corona, da ya sa aka rufe makarantu, shi ya ja hankalin matashin ya kuma yi amfani da wannan damar wajen fara wannan sana'a, wadda dama yana da ilimi a fannin sarrafa hatsi zuwa gari.
Hada karatu da sana'a babban kalubale ne da Usman Abubakar Rimi ya ce yana fuskanta, sai dai kyakkyawan tsarin da ya yi na ware lokacin karatu da na sana'a ya taimaka sosai wajen tinkarar wannan kalubale.
Daga karshe dai matashin ya shawarci takwarorin sa matasa ‘yan boko da sun jingi ne dukkanin wani girman kai sun rungumi sana'a, ita ce kadai hanya tilo da mutum ka iya kai labari.