SiyasaSudan
Matsalar agaji ga mabukata a Sudan
October 5, 2023Talla
Babban jami'in ayyukan jinkai na MDD a Sudan Clementine Nkweta-Salami ya ce "muna bukatar isa ga mutane miliyan 18 da ke bukatar tallafin gaggawa, amma ba hali bisa karancin kudi da kuma rashin kariya ga ma'aikatanmu". Don haka ya yi kira da kasashen duniya su kawo karin dauki musamman kudi don a ceci al'ummar Sudan, ya yin da su kuwa masu yaki da juna ya nemi su bada sarari a kai ga mabukatan agaji.