Bakin haure na kara kwarara zuwa neman mafaka a Turai
August 25, 2015Talla
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar UNHCR ce ta sanar da hakan, inda ta ce mafiya yawan bakin hauren 'yan gudun hijira ne da ke tserewa yakin kasar Siriya. Hukumar ta UNHCR ta kara da cewa ya zamo wajibi baki dayan kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU su kasafta 'yan gudun hijirar a tsakaninsu dai-dai wa dai-da duk kuwa da cewa a kan samu iyali guda da ke da yawan gaske wadanda ke neman mafaka a lokaci guda. A cewar hukumar akallah bakin haure 300,000 ne suka ketare Tekun Bahar Rum cikin wannan shekara inda 181,500 ke kasar Girka yayin da wasu 108,500 kuma ke Italiya kana wasu dubu 10,000 sun tsallaka zuwa Macedonia. Ta kara da cewa kaso 30 cikin 100 na 'yan gudun hijirar mata ne da kananan yara.