Matsalar bakin haure a Spain
October 6, 2005Rahotanni da daminsu sun ce kusan ‚yan gudun hijira dubu daya suka kokarta tsalllakowa daga kasar Moroko zuwa tsuburin Melilla na kasar Spain dake arewacin Afurka. Amma dimbim jami’an tsaron da aka tsugunar sun samu kafar murkushe wannan yunkuri. A karkashin wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Moroko da Spain za a rika mayar da ‚yan gudun hijirar dake tsallakowa zuwa tsuburan Ceuta da Melilla nan take zuwa kasar Moroko. Kuma tun daga yau alhamis ko kuma akalla daga gobe juma’a za a fara aiwatar da wannan mataki. An ji daga bakin P/M Maria Teresa Fernadez de la Vega tana mai bayanin cewar:
Za a dauki matakan da suka dace domin mayar da bakin hauren daga inda suka fito. Za a sake farfado da aikin yarjejeniyar da aka cimma tun a shekarar 1992 nan take.
A karkashin wannan yarjejeniya dukkan ‚yan gudun hijirar da suka tsallako daga harabar kasar Moroko zuwa tsuburan kasar Spain din guda biyu, kasar ta Moroko zata sake karbarsu in har zarafi ya kama. To sai dai kuma a baya-bayan nan kasar ta Moroko tayi watsi da wannan manufa, inda kawai take karbar ‚yan kasar da aka dawo dasu gida daga Spain, amma banda ragowar bakin hauren daga sauran kasashen Afurka, wadanda a halin yanzu, kusan a kullu yaumin sai wasu daruruwa daga cikinsu sun bi dufun dare domin satar hanyar tsallakawa zuwa Spain. Ga alamu dai a yanzun kasar Moroko ta canza shawara, inda ta cimma daidaituwa da kasar Spain a game da sake farfado da aikin yarjejeniyarsu ta shekara ta 1992 da ta tanadi mayar da bakin hauren daga Ceuta da Melilla zuwa Moroko. Kazalika kasashen biyu sun cimma daidaituwa akan karfafa hadin kai tsakaninsu wajen tsaron iyaka da taimakon jinkai. To sai dai kuma karfafa matakan tsaron iyaka da karkafa shinge ba zai tsinana kome ba wajen hana tuttudowar bakin hauren kamar yadda gwamnan yankin Melilla Juan Hose Imbroda ya nunar a jiya laraba.
Wai shin haka zamu ci gaba da giggina katanga? Idan sun tsallake ta uku sai mu gina ta hudu? Wannan matakin ba zai shawo kann matsalar ba. Za a samu ci gaba ne tare da hadin kann kasar Moroko. Domin kuwa wadannan mutanen ba daga Nijeriya ne suke tsallakowa kai tsaye ba, sai dai daga harabar kasar Moroko.
Ita dai kasar Spain ba kawai so take ta ga Moroko ta sake karbar bakin hauren ba. Muhimmin abin da take bukatar gani shi ne kasar ta dauki nagartattun matakai domin karya alkadarin bakin hauren tun kafin su yunkura domin tsallakowa zuwa tsuburan na Ceuta da Melilla.