1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar cunkoson jama'a a Afirka ta fito a jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar M. Ahiwa
November 25, 2022

Batun yawan jama'a a Afirka da janye sojojin Jamus daga Mali da ma batun kwallon kafar duniya da rawar da kasashen Afirka ke yi, sun shiga cikin labaran jaridu a Jamus.

https://p.dw.com/p/4K5Dm
Hada-hada ta kan titunan birn Dar es Salaam na Tanzaniya
Hoto: DW/G. Njogopa

Za mu yaye kallabin shirin na yau da labarin da jaridar der Freitag ta buga mai taken "Tsawon lokaci Tanzaniya ke kauce wa shirin nan tsarin iyali. Yanzu yawan jama'a ya karu da akalla ninki uku".

A lokacin hada-hadar yau da kullum, unguwar Mbagala da ke birnin Dar es Salaam na cunkushe da jama'a. Motocin safa sun cika da fasinjoji fiye da kima. Jama'a na ta karo a yayin kai komo na biyan bukata. Mbagala unguwa ce da kananan ‘yan kasuwa ke gwada sa’arsu. Suna amfana da dubun-dubatar mutane da ke wucewa ta wannan unguwa a kowace rana. Amma sun koka kan yadda wannan unguwa da ke cikin birni ke fama da cunkoson ababen hawa, da karuwar aikata kananan laifuka, da tarin sharar da ke da illa ga lafiyarsu. Bisa kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan, yawan mutane ya karu da kashi 37 cikin 100 tun daga shekarar 2012. Kuma ana sa ran samun karuwar kashi biyu zuwa uku a kowace shekara har zuwa shekara ta 2050. Don haka, Tanzaniya na daya daga cikin kasashe takwas da ke da alhakin fiye da rabin karuwar mutanen cikin shekaru talatin masu zuwa. Biyar daga cikin wadannan kasashe suna nahiyar Afirka.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz cikin sojojin Jamus a yankin Sahel
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Sojojin Jamus za su fice daga Mali nan da shekara ta 2024, abun jira a gani shi ne makomar tawagar Majalisar Dinkin Duniya bayan janyewar. Da haka ne jaridar Süddeutsche Zeitung  ta bude labarinta. Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta sanar da cewa Jamus za ta fadada ayyukanta a yankin Sahel, duk kuwa da shawarar janyewar rundunar Bundeswehr daga rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA a Mali nan da tsakiyar shekara ta 2024. A yayin muhawarar kasafin kudi a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, ministar ta ce gwamnati ta yanke shawarar cewa za ta sake tsara ayyukan da suke yi a wannan yanki mai fama da rikici, tare da abokan huldarsu na kasa da kasa. Sai dai Baerbock ta nuna cewar Jamus za ta ci gaba da kasancewa amintacciyar aminiya wadda za ta raka Mali zuwa zabenta a watan Fabrairun 2024 kamar yadda aka tsara, tare da gargadin cewar duk wani yunkuri na dage zaben a bangaren gwamnatin rikon kwarya na sojoji ba zai sa a tsawaita aikin sojin Jamus din ba.

'Yan kasar Senegal bayan sun lallasa kasar Qatar
Hoto: Petr Josek/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung sharhi ta yi  game da gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar. Jaridar ta ce kungiyoyin Afirka suna son su tsara wasan kwallon kafa na karni na 21, kuma gasar cin kofin duniya a Qatar wani muhimmin zakaran gwajin dafi ne ga masu horar da 'yan wasan. Ana ta cece-kuce kan ‘yancin kai da kuma amincewa da rashin nasara a wannan gasar cin kofin duniya, wanda tun da dadewa ya yi mummunar illa ga wannan gasa. Amma muhawarar da ake yi a 'yan kwanakin nan ita ce, fafatawar da aka shafe shekaru ana yi a fagen wasan kwallon kafa da ya bayyana cikin kwanaki na farko na gasar, ba wai rashin cikar burin 'yan wasan kwallon kafa na nahiyar Afirka kadai ba; har ma da masu horar da su. To sai dai a karon farko tun bayan da aka kirkiro gasar cin kofin duniya shekaru 100 da suka gabata, dukkan mahalarta gasar za su shiga ne bisa ga jagorancin masu horar da su da ke da tushe a kasar da za su sanya tambarin kungiyarsu a kirji a makonnin gasar ta Qatar. Wannan sabon babi ne a tarihin kwallon kafa musamman ma ga tawagar Afirka.