Matsalar fasa kwaurin hauren giwa a Togo
January 29, 2014Talla
'Yan sanda a ƙasar Togo sun kama mutane uku da aka zarga da yin safarar kimanin ton biyu na hauren giwa. Jami'an gwamnati suka ce an samu kayanne cikin buhunna a wata kwantaina da aka shirya turawa zuwa ƙasar Vietnam. Kayan da aka kama ya nuna an kashe giwaye 230, wanda shine kamun hauren giwa mafi girma da aka taɓa samu a yakin ƙasashen yammacin Afirka. A 'yan shekarunnan dai, ƙasar Togo ta ƙaddamar da yaƙi da masu fasa ƙwaurin hauren giwa, lamarin ƙasar ta yi suna a kai tun shekaru.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu