120911 Griechenland Umschuldung
September 13, 2011Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi watsi da raɗe-raɗin da wasu 'yan siyasar ƙasar ke yi cewa bisa ga dukkan alamu ƙasar Girika na dab da talaucewa. Tambaya dai ita ce shin mai zai faru idan har ƙasar ta Girika ta gaza biyan basussukan dake kanta? Babu wanda zai iya hasashen tasirin da talaucewar Girika zai yi. Wasu ƙasashe kamar Argentina sun taɓa talaucewa, amma ba a taɓa fuskantar barazanar talaucewar wata ƙasa, memba a wata gamaiyar takardun kuɗaɗe ba. Mohammad Nasiru Awal na ɗauke da ƙarin bayani.
A tarihi ba bu wani misali na irin wannan talaucewa. Wataƙila saboda haka ne ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble ya bari ƙwararrun masanansa yin wani nazari da fatan ƙara samun masaniya.
A lokaci guda kalaman game da barazanar talaucewa ya janyo rashin tabbas a kasuwannin hada-hadar kuɗi, kuma kamar wani wahayi, hakan ta ƙara tabbatar da yiwuwar aukuwar hasashen. An jiyo ministan tattalin arzikin Jamus Philip Rösler yana mai cewa.
"Bai kamata a hana duk wani tunani ko furuce furuce da zumar daidaita darajar takardun kuɗin Euro ba. A matakin ƙarshe hakan kuwa ya haɗa har da lokacin da za a gano hanyoyi mafi dacewa na daƙile barazanar talaucewar wata ƙasa."
Shi ma Firimiyan jihar Bavariya Horst Seehofer murna ya yi ganin yanzu an fito fili ana bayyana irin wannan tunani.
To sai dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi watsi da jitajita game da yiwuwar talaucewar ƙasar ta Girika tana mai cewa hakan na da alaƙa da kuɗin Euro da kuma makomar tarayyar Turai. Ta ce kamata yayi a yi takatsantsan game da kalaman da ake furtawa, abin da ba a buƙata shi ne shiga wani yanayin rashin tabbas da fargaba a kasuwannin kuɗi.
"Za mu ci gajiyar wata gamaiyar kuɗi ta ƙasashe 17, idan dukkanmu muka yi aikin tabbatar da ƙarfin Euro, kuma muka hana aiwatar da wasu aikace-aikace na babu gaira. Saboda haka muhimmin abu shi ne hana shiga wani matsayi na rashin iya biyan bashi, domin matsalar ba Girika kaɗai ta shafa ba, ta shafe mu gaba ɗaya."
Tuni dai kasuwanni suka fara mayar da martani inda a Turai baki ɗaya aka samu faɗuwar maki a kasuwannin hannayen jari. Sannan darajar takardun kuɗin Euro kuma ta yi ƙasa idan aka kwatanta da dalar Amirka.
Kasuwannin dai na buƙatar kariya domin idan Girika ta gaza, to za su yi asarar wani kaso na kuɗaɗen da ƙasar ta ranta. Ƙasashe masu amfani da Euro sun ba wa Girika basussukan dubban miliyoyi, saboda haka idan kuɗaɗe suka salwanta, to kenan basussukan da za su hau kan waɗannan ƙasashe za su wuce misali, inji Stefen Homburg shugabar cibiyar nazarin harkokin kuɗi da na tattalin arziki dake birnin Hannover.
"Idan aka kai wannan matsayi kamar yadda da ma nake sa rai cewa wani lokaci Girika za ta ce ba za ta iya biyan basussukan ba, bashin dake kan Jamus zai ƙaru matuƙa, kuma zai zama haɗari ga ƙarfin ƙasar na zama wata jingina ga wasu."
Burin wannan kace-nacen game da talaucewar Girika shi ne ƙara matsin lamba ga gwamnati a birnin Athens domin ta ƙara ɗaukar matakan tsuke bakin aljihu sannan a lokaci guda ta ƙara yawan kuɗaɗen shiga, ko kuma ƙasashen kuɗin Euro da babban bankin Turai da kuma asusun IMF su ƙi ba ta tallafin ceto na gaba.
Mawallafa: Andreas Becker/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala