1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin lantarki a kasashen Afirka

Gazali Abdou Tasawa
May 22, 2019

Rahoton bincike ya ce mutane kimanin miliyan 650 musamman a kasashen Afirka na Kudu da Sahara za su ci gaba da fama da rashin lantarki a gidajensu nan zuwa 2030.

https://p.dw.com/p/3IrWR
Afrika Elektrizität Elfenbeinküste Stromausfall
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wani rahotan binciken hadin gwiwa da wasu kungiyoyi biyar na kasa da kasa suka fitar a wannan Laraba ya yi gargadin cewa mutane kimanin miliyan 650 ne za su ci gaba da rayuwa babu lantarki a duniya nan zuwa shekara ta 2030 musamman a kasashen Afirka na kudu ga Sahara idan dai magabatan ba su dauki kwararran matakai ba. 

Sai dai Kungiyoyin biyar da suka hada da Hukumar Makamashi ta Duniya da MDD da kuma Bankin Duniya sun ce duk da haka adadin mutanen da ke rayuwa babu wutar lantarki ya ragu daga mutun miliyan dubu da 200 a shekara ta 2010 zuwa miliyan dubu daya a shekara ta 2016 zuwa miliyan 840 a shekara ta 2017.

Rahoton ya ce Kasashen Indiya da Bangladeshe da Kenya da Bama na daga cikin jerin kasashen da suka samu ci gaba a fannin samar da lantarkin daga shekara ta 2010 zuwa yanzu. 

Amma kasashen Afirka na Kudu ga Sahara da kuma wasu na nahiyar Asiya sun sune suka fi fuskantar komabaya inda mutane kusan miliyan dubu uku ke rayuwa babu lantarki a shekara ta 2017 adadin da ka iya karuwa nan zuwa 2030.