1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar matatun mai na boge a Najeriya

Ramatu Garba Baba M. Ahiwa
August 1, 2022

Kaso guda cikin uku na albarkatun man Najeriya na karewa a matatu na boge a yankin Naija Delta, inda yadda matasa ke fasa bututu da sunan maganta zaman kashe wando.

https://p.dw.com/p/4Exzr
Umweltverschmutzung im Niger Delta
Hoto: picture alliance/AP Photo

Wasu daga cikin jami'an tsaron Najeriya na amfani da gatari don farfasa wasu matatun mai na boge da suke bankadowa a wani wuri a yankin Naija Delta, daga bisani ma sun cinnawa matatar man wuta. Da ma dai a kullum gwamnatin kasar na cewa tana aiki dare da rana don kawar da su amma har yanzu abin ya faskara.

Tun daga watan Afrilun da ya gabata, akalla mutane 100 ne suka rasa rayukansu a jerin samamen da jami'an tsaro ke kai wa kan barayin man. Duk da wannan namijin kokarin, babu alama hakar gwamnati na cimma ruwa in ji wani jami'i mai suna  Solomon Diri-Ogbere.

Yankin da ake tafka wannan ta'asar na fama da matsaloli na malalar mai da ta gurbatar ruwa da gonaki, wasu ma na danganta yawan rashin lafiya da mazauna kauyukan yankin ke fama da su da ayyukan masu fasa bututan man.

Nigeria Ölverschmutzung Öl Ogoniland
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb/M. A. Johnson

Daya daga cikin masu wannan sana'ar da ya nemi a sakaya sunansa ya yi wa DW bayanin dalilansa na kasa daina satar man.

''Ba za mu ci gaba da rayuwa kara zube a ce ba mu da abin yi ba, saboda haka mu wannan sana'a ce a gare mu da muke samun kudin biyan bukatunmu. Mun san sana'ar na tattare da hadari saboda haka muna taka tsantsan''

Wadannan matatun man na boge, su suke samar wa jama'a a yankin makamashin girki kamar kananzir inda suke sayar wa jama'a a cikin farashi mai rahusa. Abin da ke ci gaba da daure wa da dama kai shi ne yadda  Najeriya ta gaza samar da halastattun matatun mai a yankin duk da kasancewar ta kasa mai albarkatun man na fetur; kuma jama'a na ci gaba da fama da matsalar karancin man.

Masu fafutika na ganin da taimakon gwamnati, yankin Bayelsa ka iya zama cibiyar da za a rika haka da ma tace mai. Suna son ganin gwamnati ta samar da halastatun matatun mai a yankin tare da bai wa ma'aikata horo na musanman. Sai dai kafin nan, 'yan bunburutun za su ci gaba da sana'arsu ta fasa matatun man gwamnati duk kuwa da ire-iren haduran da ke tattare da wannan bakar sana'a.