1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Burundi yayi barazanar korar alkalai

Ramatu Garba Baba
August 25, 2021

Shugaba Evariste Ndayishimiye yayi barazanar sallamar daukacin alkalan kotun kasar saboda zargin cin hanci da rashawa da suka hana kasar ci gaba.

https://p.dw.com/p/3zUV7
Burundi Bujumbura | Evariste Ndayishimiye, Präsident
Hoto: Bujumbura Amida Issa/DW

Shugaban kasar Burundi yayi barazanar sallamar daukacin alkalan kotun kasar saboda zargin da ake musu na cin hanci da rashawa, a fusace, Shugaba Evariste Ndayishimiye ya soki alkalan da ya ce, suna da hannu dumu-dumu a hana ci gaban kasar saboda yadda suka hada kai da 'yan siyasa wajen yi wa kasar ta'annati.  

Ya baiyana halin da kasar da ke mataki na goma a cikin jerin jadawalin kasashe matalauta a duniya, da abin kunya inda masu zuba jari daga kasashen waje ke kaurace mata, saboda matsalar da ta yi wa Burundi katutu.

Tun bayan dare madafun iko a watan Yunin bara, shugaban ya soma yakar rashawa inda har ta kai, ya sallami manyan jami'an gwamnati uku da ma'ajin kudi na wasu gundumomi sha tara bisa laifin cin hancin. Ana dai ganin matsalar ce ta hana kasar ci gaba, inda al'ummarta ke fama da tsananin talauci.