Maza masu matsalar rashin haihuwa
July 26, 2022Sabon binciken kwararru ya nunar da cewa, akwai sama da kashi 40 cikin 100 na maza masu fama da matsalar rashin haihuwa musamman saboda wasu cututtuka, sai dai saboda fargabar tsangwama wasu da dama na karyata halin da suke ciki su kuma dora matsalar kan mata da suke rayuwar auratayya tare.
Wani rahoto a kasar Yuganda, ya nuna adadin maza da ke fama da mastalar rashin haihuwa na karuwa, sai dai mafi akasari suna bijirewa binciken tare da dora matsalar kan mata da suke zamantakewa tare, saboda tasirin camfi. Yuganda, na daga cikin kasashen Afirka da camfi ke tasiri a tsakanin al'umma.
A kasashe masu tasowa da kimiyya ke baya, an fi danganta matsalar rashin haihuwa ga mata, sai dai a yanzu lamarin na kara fitowa fili cewa maza ma suna da shi. Duk da wannan matsala, kwararrun likitoci na cewa wasu matsalolin, ana iya shawo kansu muddin aka yi saurin ganosu.