1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tattalin arziki a ƙasar Girka

June 20, 2011

Ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai sun sha alwashin tallafa wa Girka amma bisa sharaɗin majalisar dokokin ƙasar ta amince da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.

https://p.dw.com/p/11fLm
Hoto: fotolia

Ministocin kuɗi na ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai sun amince da shirin tallafa wa ƙasar Girka da ƙarin kuɗaɗen rance a zagaye na biyu domin ceto ƙasar daga matsalar tattalin arzikin da ta samu kan ta a ciki sakamakon basussukan da suka yi mata katutu. Ministocin wanɗanda suka amince su ba da kuɗaɗen bashi sun ce dole ne ƙasar ta rage yawan kuɗaɗen da take kashewa da Euro biliyan 28.

Sannan kuma ta ce tilas ne majalisar dokokin ƙasar ta Girka ta kaɗa ƙuria'a amincewa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati, waɗanda suka haɗa da rage kuɗaɗen albashi da na pansho da ƙaddamar da shirin sayar da hannayen jari na kamfanoni mallakar gwamati akan kuɗaɗen bashin na biliyan 12 na kuɗin euro da za su samu. Ministocin waɗanda ba su sa hannu ba tukuna akan yarjejeniyar sun ce za su duba yadda za su cimma daidaito da kamfanoni dake bin ƙasar Girka bashi domin su ɗage lokacin da ƙasar za ta biyashe su. Ministan kuɗi na ƙasar Jamus Wolfgang Schäuble da ya halarci zaman taron na Luxemburg ya furta cewa a shirye ake a tallafa wa ƙasar ta Girka idan har za ta ƙaddamar da sauye sauye masu ɗorewa don ci gaba.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal