1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro a yammacin Afirka

Umaru AliyuJuly 10, 2014

A taron Kungiyar Gamayyar Kasashen Yammacin Afirka da aka yi a Ghana, shugabanin sun bayyana takaicinsu kan matsalar tsaron da ke kawo koma baya musamman a tattalin arziki da yanayin zamantakewar yankin

https://p.dw.com/p/1CaQf
Ecowas Afrika Ökonomie Treffen Gipfel Abidjan Elfenbeinküste
Hoto: Reuters

A taron Kungiyar Gamayyar Kasashen Yammacin Afirka karo na 45 wanda ke gudana a Accra na kasar Ghana, shugabanin kasashen sun duba ayyukan kungiyar na tsawon watanni shiddan da suka gabata, tare da batun tabarbarewar tsaro da ya yi wa wasu kasashe mambobinta katutu yanzu haka.

Kasancewar an gudanar da taron gaggawar a watan Mayun da ya gabata, inda shugabannin suka mayar da hankali kan batun yaki da safarar miyagun kwayoyi, aiwatar da ayyukan ashsha da dai sauransu.

A taron na wannan karon wanda ya sami halartar kusan dukkanin shugabanin kasashe mambobin kungiyar tare da wasu wakilanta, batun samar da ingantaccen tsaro a Najeriyar ne ya fi daukar hankali dangane da halin ni 'ya su da take ciki ya zuwa wannan lokkacin, musamman na batun kame yaran nan 'yan matan Chibok wadanda har yanzu ba a sami cikakken labari kan inda suke ba. Na tambayi Salamatu Hussaini Suleimana wacce ita ce kwamishanar harkokin siyasa da tsaro da zaman lafiya ta ECOWAS kan irin ci gaban da aka samu.

Ecowas Afrika Ökonomie Treffen Gipfel Abidjan Elfenbeinküste
Shugabanin Afirka a taron da suka yi a watan Janairun baraHoto: picture-alliance/Landov

Taron ya dauki matakan inganta kasuwanci

Batun kasuwanci dai na daya daga cikin ababen da ke ci wa kasashen mambobi tuwo a kwarya domin akwai batun biyan dimbim haraji, daukan lokaci wajen binciken kayayyaki gabanin gabatar da takardun karesu tare da kafa shingaye barkatai wanda ke sanadiyyar rashin shiga kayyakin da ake saraffasu a kasashen mambobi a kasuwanin duniya domin kafin a kare amma nan bada jimawa ba zaa kawo karshen wannan batu a cewar Chairman Ecowas kuma shugabann kasar Ghana John Mahama.

"Mun dai samu bayyanai da dama daga wurin wadanda aka dora wa batun duba wannan lamari tare kuma da samun ci gaba kan biyan haraji na bai daya tsakanin kasashe mambobi wato Common External Tariff wanda ake sa ran aiwatar da shi a ranar daya ga watan Janairun shekara ma kamawa. Ina kuma tunasar da shugabanin kasashen mambobi cewar su tabbatar an wayyar da kan jamaa musamman 'yan kasuwa kan wannan batun samar da haraji na bai daya."

Ga dukkan alamu dai yanzu kam Kungiyar ECOWAS ta kama hanyar ci gaba domin kuwa nan ba da jimawa ba za ta samar wa kasashe mambobinta kati na bai daya, wanda zai warware matsalar wulakanci da cin hanci a iyakokin kasashen yankin.

Mawallafiya: Rahmatu Mahmud Abubakar Jawando
Edita: Pinado Abdu Waba