1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai na fuskantar gagarumar matsalar 'yan gudun hijira

Lateefa Mustapha Ja'afarDecember 23, 2015

Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa ta ce sama da 'yan gudun hijira da bakin haure miliyan daya ne suka tsallaka kasashen nahiyar Turai a wannan shekarar.

https://p.dw.com/p/1HS2r
Karuwar 'yan gudun hijira da bakin haure a Turai
Karuwar 'yan gudun hijira da bakin haure a TuraiHoto: Reuters/L. Balogh

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da wannan adadi, inda babban jami'in hulda da kafafen yada labarai na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar William Spindler da ya tabbatar da hakan ke cewa:

"Wannan babbar matsala ce da duniya baki daya ke fuskanta tsahon shekaru. Kuma a yanzu ne kawai da matsalar ta shafi nahiyar Turai, Turan ta mayar da hankali a kai. Tsahon shekaru mutane na tserewa yaki a Siriya da sauran wuraren da ke fama da rikici, amma a wannan shekarar da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar na kwarara zuwa Turai. Mun samu bayanan da ke cewa sama da mutane miliyan daya ne suka isa Turai cikin wannan shekarar kawai."

Kiyasi dai ya nunar da cewa yawan 'yan gudun hijira da suka shiga Turai wannan shekarar kadai sun ninka na bara har sau uku, kana wadanda aka samu rahoton rasuwarsu a kan hanyarsu ta shiga Turan ma ya fi na shekarar da ta gabata ta 2014.