EU za ta gina matsugunan 'yan gudun hijira
October 26, 2015'Yan gudun hijirar dai na amfani da kan iyakokin kasashen na yankin Balkan wajen shiga kasashen da suka ci gaba a nahiyar Turai, hakan ce ma ta sanya yunkurin gina matsugunan a wani mataki na dakile matsalar kwararar 'yan gudun hijirar da kan iyakokin yankin gabashin Turai ke fuskanta. Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ne ya sanar da hakan bayan da suka kammala wata tattaunawa ta gaggawa kan matsalar 'yan gudun hijirar a birnin Brussels. Shugabannin kasashe 10 na kungiyar Tarayyar Turan da suka hadar da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da kuma shugabannin kasashen da basa cikin kungiyar ta EU da suka hadar da Albaniya da Sabiya da kuma Macedonia ne suka gudanar da wannan taro na gaggawa a karshen mako biyo bayan gargadin da kaashen Bulgeriya da Romaniya da kuma Sabiya suka yi na rufe kan iyakokinsu da ke cunkushe da 'yan gudun hijirar da suke son tsallakawa kasashen da ke da karfin tattalin arzki a nahiyar ta Turai.