1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Siriya na fuskantar yunwa

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 4, 2016

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Yacoub El Hillo ya ce, ya zamo wajibi a kai kayan agaji yankunan Madaya da Zabadani da Foua da kuma Kafraya da ke kasar.

https://p.dw.com/p/1JJ0D
Yadda yaki ya dai-daita Siriya
Yadda yaki ya dai-daita SiriyaHoto: picture-alliance/AA/. Eby Leys

El Hillo wanda ke yin jawabi daga Damascus babban birnin kasar ya nunar cewa in kuwa ba haka ba, al'ummar da ke yankunan za su fuskanci matsananciyar yunwa. Rahotanni sun nunar da cewa Madaya da Zabadani, da ke wajen birnin Damascus na zagaye ne da dakarun gwamnati yayin da 'yan tawayen kasar suka zagaye garuruwan Foua da Kafraya da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar. Tun dai cikin shekarar da ta gabata ne ake fargabar cewa yankunan suna killace, kuma ba kasafai ake kyale ayarin masu ba da agaji su shiga cikinsu ba. Koda cikin watan Janairun da ya gabata ma dai, sai da kungiyar Likitoci na gari na Kowa ko kuma Doctors Without Borders da turancin Ingila suka sanar da mutuwar mutane 16 a Madaya, abin kuma da El Hillo ya bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin biyu da kada su sake hakan ta sake faruwa.