1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsaloli game da zabukan 2015 a Najeriya

Uwais Abubakar Idris/ASJanuary 27, 2015

Tawagar Kungiyar Tarrayar Turai ta EU da ke sa ido kan zaben Najeriya ta ce ta damuwa a kan matsaloli ga zaben kasar tun daga zaben fidda gwani da rashin aiki da doka yadda ya dace.

https://p.dw.com/p/1ERFN
Wahlen Nigeria Attahiru Jega
Hoto: AP

Tawagar Kungiyar Tarayyar Turai din ta ce wadanan matsaloli ka iya kasancewa babban cikas ga zaben na Najeriya. Shugaban tawagar Santiago Fisas ne ya bayyana hakan wanda ya ce a wannan karon kungiyar ta shirya turo tawaga fiye da kowane lokaci zuwa Najeriyar domin tabbatar da sa ido a kan zaben da ake sa ido a kansa a kasar da kasashen duniya.

Afrika Wahl in Mali 15.12.2013
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce ta shirya don yin sahihin zabe.Hoto: AFP/Getty Images

Mr. Fisas ya ce "tsarin zaben na Najeriya na cike da matsalolin gaske domin kuwa jam'iyyun sun kasance masu kaka gida a daukacin harkar batun tsayawa takara, babu wata dama ga dan takara mai zaman kansa ya tsaya zabe a Najeriya domin kuwa dokoki ba su da wannan tanadin bai. Ita kanta hukumar zaben kasar bata da ikon aiwatar da duk wani hukunci kana tsadar da ke tattare da tsayawa takara a ta taimaka wajen hana wasu 'yan kasar shiga zabe''.

Duk da cewa a bana yawan wakilan da za su sa ido a zaben na Najeriya daga kungiyar sun karu sosai, amma tawagar ta ce ba za ta iya tura koda wakili guda ba zuwa yankin arewa maso gabashin Najeriya saboda yanayi na rashin tsaro da ake fama da shi, sai dai ba kaman sauran kungiyoyin kasashe da ke sa ido a kan zaben na Najeriya ba, tawagar EU din za ta sa ido a kan yadda kafofin yada labaru ke bada rahotanin da suka shafi zaben.

Wannan dai ba shi ne karon farko da tawagar ke sa ido a zabe tare da bada shawarwari ba to amma ya zuwa yanzu guda nawa ne gwamnatin Najeriyar ta aiwatar a cikin shawarwarin da suka bayar a zaben 2011? Wannan ita ce irin ayar tambaya da 'yan kasar da su kansu masu sanya idanu kan zaben na Najeriya ke yawan azawa. Kimanin kasashe 25 na kungiyar ta EU ne za su aiko da wakilai don sa ido baya ga wanda za su je kallon zaben daga Norway da Switzerland.

Symbolbild Nigeria Polizei
Rashin tsaro na barazana ga gudanar zabe a arewa maso gabashin Najeriya.Hoto: imago/Xinhua