Sarkakiya kan kafa gwamnatin Thailand
May 16, 2023A kasar Thailand jam'iyya mai ra'ayin gaba-dai gaba-dai da ta samu galibin 'yan majalisa da shugabanta Pita Limjaroenrat suna ci gaba da fuskantar sarkakiya wajen kafa gwamnati bayan babban zaben da ya gudana a karshen mako. Shi dai Pita Limjaroenrat yana fata kan zaman firamnistan kasar na gaba.
Jam'iyyar ta Move Forward wadda ta fito da batun sarauta kiri-kiri lokacin yakin neman zabe tana ci gaba da gamuwa da cikas ganin duk sauran jam'iyyun suna cikin wadanda suka dade ana damawa da su kan harkokin kasar. Kuma ana gani tilas sabuwar jam'iyyar da ta samu gagarumin goyon bayan jama'a ta sassauta matsayi kan batutuwa da dama kafin ta samu kawance kafa gwamnatin Thailand ta gabata, kasar da ta saba da rudanin siyasa da juye-juyen mulki na sojoji shekara da shekaru.