1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Mata na fataucin kwayoyi a Jamhuriyar Nijar

Issoufou Mamane SB/MAB
February 27, 2024

Wani abunda ke daukar hankali Jamhuriyar Nijar shi ne yadda mata ke fataucin kwayoyi da dangin kayan maye wanda ya sa hukumomin kasar suka dauki matakin farautar matan dake wannan sana'ar ta safarar kwayoyin.

https://p.dw.com/p/4cwWM
Kwayoyi
KwayoyiHoto: DW

A Jamhuriyar Nijar wani abin da ke zaman kalubale ga al'ummar kasar shi ne yadda sannu a hankali mata ke mayar da hankali ga safara da fataucin kwayoyi da wasu kayan maye a 'yan shekarun baya-bayan nan, sana'ar da ke tattare da hadari wadda a can baya ke zaman abun dogaro ga mazaje.

Jami'an tsaron a jihar Tahoua sun kama wasu matan dauke da miyagun kwayoyi da ake zarfi suna safara zuwa wasu sassan kasra da ma kasashen ketere.