'Yan awaren Kamaru sun jefa matafiya cikin kasada
September 17, 2024Matuka motocin sun tsayar da jigirlar matafiya da dakon kaya a yankin tsak sakamakon barazanar 'yan bindiga wanda daya daga cikin matuka motocin ya shaida wa DW cewa ya yi asarar motarsa guda a 2019 da 'yan bindiga suka kona kurmus sakamakon rashin mutunta dokar da suka sanya ta tilasta zaman gida da hana zirga-zirgar ababen hawa a fadin yankin.
Karin Bayani: Najeriya: Harin 'yan Ambazoniya na Kamaru
Yanzu haka motocin sufuri da dama na ajiye sun cika wajen ajiye motoci da ke tashar na zuwa kudu maso yammaci a garin Bonaberi karamar hukumar Douala na hudu. Wannan babbar matsala ce ga direbobin saboda ba su da wata hanyar shigar kudi duba da abubuwa da ke kansu kamar inshora da biyan haraji da sauransu ga hukuma.
Baya ga direbobin motocin sufuri na fasinja, manyan kamfanoni kamar CDC na ayyukan noma sun rage direbobin manyan motocin dakon kaya sakamakon barazanar 'yan bindigan domin a shekarar 2022 yan awaren sun yi awon gaba da direbobin kamfanin guda 8 lokacin da suke kan hanyarsu tsakanin garin Tiko da Douala cibiyar kasuwancin Kamaru.
Tattalin arzikin kasar ya durkushe sosai sakamakon rikici tsakanin dakarun Yaounde da 'yan aware da suka dauki makamai a 2017 domin kafa kasarsu mai cin gashin kanta sai dai a hanlin yanzu rikici ya canza salo saboda fararen hula 'yan awaren da jami'an tsaron ke musgunawa mafi yawan mutanen da suka mutu fararen hula dubbai kuma sun yi gudun hijira zuwa sassan kasar musamman ma Douala.