Lafiya
Somaliya tana cikin matsanancin yunwa
October 18, 2022Talla
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce farin da ake fuskanta a kasar Somaliya ya kasance mafi muni ga kasar cikin shekaru 50 da suka gabata. A wannan Talata mai magana da yawun asusun, James Elder ya ce ana bukatar kimanin kudi Dalar Amirka milyan dubu-biyu saboda a tunkari matsalar.
Jami'an asusun na UNICEF ya kara da cewa a watan Agusta da ya gabata kadai kimanin yara 44,000 aka kwanatar a asibiti sakamakon matsananciyar yunwa. Kimanin mutane milyan-takwas kusan rabin mutanen kasar ta Somaliya farin ya shafa a cewar Majalisar Dinkin Duniya, dama kasar tana cikin tashe-tashen hankula na tsageru masu kaifin kishin addinin Islama.