1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayi duniya game da kisan gilla a Pakistan

January 5, 2011

Kisan gilla da aka yi wa Salman Taseer gwamnan Punjab na ta shan tofin Allah tsine daga ko ta ina a ciki da wajen ƙasar Pakistan.

https://p.dw.com/p/ztks
Salman Taseer da wakilin DWHoto: DW

Ƙasar Amirka da kuma ƙungiyar Gamayyar Turai na cikin ruƙunin waɗanda suka yi tur da kashe gwamna Salman Taseer da mai tsaron lafiyarsa yayi. Suna masu cewa wannan ba ƙarin koma baya ba ne a Pakistan, kasancewa ya daɗe ya na bayar da gudun mawa wajen tabbatar da ci gaba da kuma kwanciyar hankali a ƙasar. Abin takaicin ma a cewar fadar mulki ta Washington adawarsa da ya nuna a fili game da tsaurin ra'ayin addini ne ya sa aka yi masa luguden wuta. A saboda haka ne Kantomar da ke kula da harkokin ƙetare na Eu wato Catherine Ashton ta yi kira ga hukumomin Islamabad da su iya ƙoƙarinsu wajen gano duk waɗanda suka kitsa wannan ɗanya tare da gurfanar da su gaban ƙuliya. Wannan dai shi ne kisan gilla mafi muni da aka fiskanta a fagen siyasar Pakistan tun bayan na tsofuwar firaministan ƙasar wato Benazir Bhutto a watan disemban 2007. Daidai da Mahmood Shafqat da ke zama masharhanci harkokin siyasar Pakistan sai da ya bayyana takaici da kuma ɓacin ransa game da kisan Taseer.

Pakistan Gouverneur Salman Taseer ermordet
Gwamnan Punjab da aka kasheHoto: DW

"Mutun ne mai ƙarfin zuciya. Mutan ne da baya ga ƙarfin zuciyar ma, ke da nuna juriya. Kai tsaye ya ke bayyana abin da ya tunawa. Wannan wani abin ban tausayi ne, kuma rashi ne babba."

Salam Taseer ya daɗe da fara adawa

Shi dai Salman Taseer ya daɗe da ƙalubalantar manufofin gwamnatoci da ke riƙe da madafun iko. Ko bayan naɗa shi gwamnan yankin Penjab shekaru biyun da suka gabata, sai da yayi ta sa in sa da gwamantin Nawaz Sharif. A wannan karon ma duk da kasance ƙusa a cikin jam'iyar PPP mai mulki, ya bi sahun ƙungiyoyi masu kare hakkin bil Adam wajen nuna cewa kafa doka da ta shafi ɓatanci ga addinin musulunci bai dace a ƙasar da ke da mabiya addinai barkate ba, ciki kuwa har da kiristanci da kuma addinin hindu. Amma kuma uwar jam'iyar ta PPP da ke mulki da kuma wasu jam'iyun da ke da rajin tabbatar da dokar musulunci a ƙasar da suka danganta shi gwamnan da baragurbi, suka nemi kawar da shi saboda ƙarfin faɗa a ji da ya ke da shi a cikin jam'iyar da ma dai tsakanin mutanen Pakistan. Alhali a cewar Mahmood Shafqat , wanda kuma mamba ne na jam'iyar PPP da ke mulkin Pakistan, banbancin abin da suke faɗa bai taka kara ya karya ba.

Anschlag auf Cricket Team in Pakistan
Salman Taseer kafin mutuwarsaHoto: AP

"Matsayin da mutane ke ɗauke, shi ne yadda aka tsara wannan doka zai iya haifar da tauye hakki. A saboda haka nauyin mu ne mu tabbatar da cewa ba a yi amfani da ita wajen cika wani burin siyasa ba. Na yi imanin cewa yunƙurin da Salman Taseer ya yi ta yi ke nan. Amma kuma mutane da ba su da zurfin tunani, waɗanda tsaurin ra'ayin adduni ya rufe musu ido suka danganta ta shi da mai adawa da addinin musulunci."

Jana'izar Salam Taseer a yau

Baya ga kasancewarsa Salman Taseer da aka yi wa lugunde wuta ɗan siyasa, ya mallakin kanfanin sadarwa da kuma wata jarida da ake wallafawa a kullu yaumin mai suna "The liberal Daily Times". Zaman makoki na kwanaki uku firaministan Pakistan Youssouf Raza Gilani ya keɓe a gwamnatance saboda ƙima da Salman Taseer ke da shi a idanun gwamnatinsa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu