Matsayin Amurika a game da rikicin nuklear Iran
February 24, 2007Mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney ya ki ya ce uffan a game da yiwuwar daukar matakan soja akan kasar Iran idan har ta ki ta dakatar da shirinta na nukiliya. A lokacin wani taron manema labarai na hadin guiwa tare da piraministan Australiya John Howard a birnin Sidney, Dick Cheney ya nuna cewar zai zama babban kuskure idan har aka kyale kasar Iran ta mallaki makaman nukiliya kuma har yau akwai shawarwari daban-daban da aka gabatar akan wannan batu. Daga baya-bayan nan ne hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta gabatar da rahoton dake cewar kasar Iran bata yi biyayya ga wa’adin da kwamitin sulhu na MDD ya tsayar mata domin ta dakatar da sarrafa sinadarin uranium ba. A yau in an jima ne kuma mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amurka Nicholas Burns zai sadu da jami’an diplomasiyyar Turai a birnin London domin tattauna matsalar.