1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin kasashen Turai kan zaben Girka

Mouhamadou Awal BalarabeJuly 6, 2015

Wasu kasashen Turai sun nuna wajibcin jerawa da Girka a rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin Euro yayin da wasu ke neman a dakatar da ita daga gamayyar.

https://p.dw.com/p/1Fte2
Hoto: ap

Har yanzu dai shugaban rukumin kasashen da ke amfani da kudin Euro Jereon Dijsselbloem ya na kan bakarsa cewar sakamakon kuri'ar raba gardama da aka samu a Girka ya dada dagula al'amura. Hasali ma ba wanda ya san alkiblar da za a dosa bayan da al'ummar Girka suka yi watsi da sharadin tsuke bakin aljuhu da TUrai ta gindaya musu kafin basu tallafin da suke bukata.

Su ma dai Kasashen Gabashin Turai suna neman a nuna rashin sani da sabo a kan Girka. Dama dai wadannan kasashe da suka hada da Estoniya da Lituaniya da kuma Slovakiya na daga cikin wadanda suka dandana matakan tsuke bakin aljuhu domin tayar da komadar tattalin arzikinsu. Ko da a yanzu ma dai suna daga cikin kasashen Turai da tattalin arzikinsu bai habaka ba sosai. Saboda haka ne suka ce ba za su karawa mai karfi karfi ba, ma'ana ba za su taimakawa Girka ba saboda ta fi su karfin tattalin arziki.

Sai dai kuma wannan mataki ya saba da matsayin hukumar zartaswa ta EU, wacce ta ce kofa a bude take ta komawa kan teburin tattaunawa da Girka duk da sarkakiyar da ke tattare da wannan mataki. Valdis Dombrovskis wanda shi ne mataimakin shugaban hukumar zartaswa ta EU ya yi tsokaci a kan wannan batu

Valdis Dombrovskis PK EU Kommission Brüssel
Mataimakin shugaban hukumar EU ya ce za su sake tattaunawa da GirkaHoto: Reuters/Francois Lenoir

"Babu wata hanya mai sauki ta warware wannan matsalar.An bata lokaci da kuma damar da aka yi ta samu. Hukumar zartaswa ta Eu a shirya take ta yi aiki da Girka. Amma fa a sani cewar hukumar ba za ta iya tattaunawa kan sabbin matakai ba sai da izinin rukunin kasashen da ke amfani da Euro ."

Ranar Talata ce shugabanin kasashen da ke amfani da Euro za su gudanar da taron koli a Bruxelles don daukan matakai kan Girka, na ci gaba da taimaka mata ko kuma fitar da fitar da ita daga Euro Zone. Dangane da hake ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nika gari i zuwa Paris na Faransa domin daukan matakan bai daya a kan wannan batu tare da shugaba Francois Hollande. Dama dai kasashen biyu wato Jamus da Faransa ne ja gaba a nahiyar Turai da ma da kasashen da ke amfani da Euro.

Ministan kudin Faransa Michel Sapin ya ce wannan keke da keken ne kawai zai iya sa a gano bakin zaren warware rikicin da ake fama da shi.

#b#"Ba za a iya magance wannan matsala ba matikar ba a yi doguwar tattaunawa tsakanin Angela Merkel da Francois Hollande ba da nufin samun mafita. Ina sake jaddada muku cewar tallafawa Girka ba batu ne da za a yi rufe-rufa a kai ba."

Su ma dai kasashen Spain da kuma Italiya suna goyon bayan ga duk wani yunkuri na sake taimakawa Girka da kudi domin ta farfado daga halin da ta samu kanta a ciki.